Você está na página 1de 2

Surah 87: Al-Ala -

[87:0] Bismi ALLAH, Alrahman, Alrahim.*

[87:1] Ka tsarkake sunan Ubangijinka Mafi daukaka.

[87:2] Wanda Ya yi halitta, sa'an nan Ya fasalta.

[87:3] Wanda Ya yi qaddara, sannan Ya shiryar.

[87:4] Kuma Wanda Ya fitar da makiyaya.

[87:5] Sa'an nan Ya mayar da ita baro mara nauyi.

[87:6] Za mu karantar da kai; saboda haka ba za ka manta ba.

[87:7] Sai abin da ALLAH Ya so; Ya san bayyane da abin da yake boye.

[87:8] Kuma za Mu nuna maka hanya mafi sauqi.

[87:9] Saboda baka, ka tunatar; watakila tunatarwa za ta yi amfni.


[87:10] Wanda ke tunani zai tuna.

[87:11] Kuma shaqiyyi, zai nisanceta,

[87:12] A sanadiyar haka zai shiga wutar da ta fi girma.

[87:13] Wurin da ba zai mutu ba a cikinta, kuma ba zai rayu ba.

[87:14] Lalle ne wanda ya tsarkaka ya rabauta.

[87:15] Da ambaton sunan Ubangijinsa, sa'an nan yana yin sallah.

[87:16] Lalle ne, kun shagala da rayuwan duniya.

[87:17] Alhali kuwa Lahira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa.

[87:18] Lalle ne, wannan yana a cikin litattafan farko.

[87:19] Littaffan Ibrahim da Musa.

Você também pode gostar