Você está na página 1de 9

‫‪Shuruddan‬‬

‫ال اله اال الله‬


© Masjid Mus'ab bn ʿUmayr, Kano, Nigeria.

Da taimako da kuma izini na Allāh wannan daftari ne da aka Masjid


Mus'ab bn ʿUmayr, Kano ta tattara. Za a iya bugawa kuma a rabã kyauta,
amma ba a yarda a siyar ta kowacce hanya domin samun riba ba.

Fassara Masjid Mus'ab bn ʿUmayr Kano Editorial.


1. Ilimi (Al-'Ilm):

Sanin ma'anarta da take dauke dashi da abinda take


korewa da abinda take tabbatarwa, wanda wannan sanin
nata shi yake kore jahilci.

﴾٨٦﴿ ‫ِإَّلا َمن َشِهَد ِباْلَحِّق َوُهْم َيْعَلُموَن‬

Allāh Madaukakin Sarki yana cewa: "Sai wanɗanda suka


shaida da gaskia (Lā ilaha ilā Allāh) una masu saninta sani
na gaskia". (Sūrah Az-Zukhruf:86)

Ma'anar saninta sani na gaskia shine: su santa da


zuciyoyinsu ba wai kawai da harsunansu ba don da mutum
zai furta ta alhali bai san ma'anarta ba to bazata amfaneshi
ba saboda bai qudurce ma'anar ta ba.

Kitāb ʿAqīdah at-Tawḥīd na Shaykh Ṣāliḥ Al-Fawzān (sh. 42-43)

2. Yaqini (Al-Yaqīn) :

Shi ne ya kasance mai fadinta yana mai yaqini akan


ma'anarta, in yana shakku akan ma'anarta to bazata
amfaneshi ba.
Allāh, Madaukakin Sarki, yace:

﴾١٥﴿ ‫ِإَّنَما اْلُمْؤِمُنوَن اَّلِذيَن آَمُنوا ِبالَّلِه َوَرُسوِلِه ُثَّم َلْم َيْرَتاُبوا‬

Kaɗai muminai sune wadanda sukayi imani da Allāh da


ManzonSa sannan basuyi kokwanto ba. (Al-Hujurāt:15)

In har ya kasance mai kokwanto to ya kasance munafiki.


Manzo ( ) yace: "Duk wanda ka hadu dashi a bayan
gininnan yana mai shaidawa babu abun bauta bisa
cancanta sai Allāh kuma yana mai yaqini acikin zuciyarsa to
kayi masa bushara da Aljanna".

To duk wanda bai samu yaqini a zuciyarsa ba bai cancanci


shiga Aljannah ba.

Kitāb ʿAqīdah at-Tawḥīd na Shaykh Ṣāliḥ Al-Fawzān (sh. 43)

3. Karba (Al-Qabūl) :

Karbar abinda wannan kalmar take hukuntawa na bautar Allāh shi


kadai da barin bautar waninsa. Duk wanda ya furta ta amma bai
karba, ko ya lazimci abinda take kunshe dashi ba to yana
wadanda Allāh yake cewa dangane dasu:

‫﴾ َوَيُقوُلوَن َأِئَّنا َلَتاِرُكوا‬٣٥﴿ ‫ِإَّنُهْم َكاُنوا ِإَذا ِقيَل َلُهْم َلا ِإَلَه ِإَّلا الَّلُه َيْسَتْكِبُروَن‬
﴾٣٦﴿ ‫آِلَهِتَنا ِلَشاِعٍر َّمْجُنوٍن‬

"Lalle suna daga cikin wadanda in akace dasu suce Lā ilaha ilā
Allāh sai suyi girman kai suna cewa yanzu sai mu bar abubuwan
bautarmu saboda wani mawaƙi, mahaukaci". (As-Safāt: 35-36)
Wannan yayi daidai da halin masu bautar ƙaburbura (yan
dariƙu) suna fadin Lā ilaha ilā Allāh amma basa barin
bautar ƙaburbura, don haka basu zama masu karbar
ma'anar Lā ilaha ilā Allāh.

Kitāb ʿAqīdah at-Tawḥīd na Shaykh Ṣāliḥ Al-Fawzān (sh. 43-44)

4. MiƘa wuya (Al-inqyād)

Miƙa wuya ga abinda take nufi. Allah Madaukakin sarki


yace:

﴾٢٢﴿ ‫َوَمن ُيْسِلْم َوْجَهُه ِإَلى الَّلِه َوُهَو ُمْحِسٌن َفَقِد اْسَتْمَسَك ِباْلُعْرَوِة اْلُوْثَقى‬

Duk wanda ya miƙa wuya izuwa ga Allah yana mai


kyautatawa to lalle yayi riƙo da igiya mai ƙarfi.
(Luƙman:22)

-Igiya mai ƙarfi: itace Lā ilaha ilā Allāh

-Miƙa wuya: shine miƙa wuya ga Allah ta hanyar


tsarkakeshi.

Kitāb ʿAqīdah at-Tawḥīd na Shaykh Ṣāliḥ Al-Fawzān (sh. 44)

5. Gaskiya (AṢ-Ṣiddīq ) :

Shi ne ya fadi wannan kalmar (Lā ilaha ilā Allah) yana mai
gaskatata da zuciyarsa, idan ya fadeta da harshensa amma
bai gaskata ta da zuciyarsa ba to munafikine maƙaryacine.
Shi ne ya fadi wannan kalmar (Lā ilaha ilā Allah) yana mai
gaskatata da zuciyarsa, idan ya fadeta da harshensa amma
bai gaskata ta da zuciyarsa ba to munafikine maƙaryacine.
Shi, Madaukakin, yace:

﴾٨﴿ ‫َوِمَن الَّناِس َمن َيُقوُل آَمَّنا ِبالّلِه َوِباْلَيْوِم اآلِخِر َوَما ُهم ِبُمْؤِمِنيَن‬
﴾٩﴿ ‫ُيَخاِدُعوَن الّلَه َواَّلِذيَن آَمُنوا‬

"Daga cikin mutane akwai wanda yake cewa munyi imani


da Allāh da ranar lahira amma ba muminai bane suna
yaudarar Allah da wadanda sukai imani".

Izuwa fadinSa:

﴾١٠﴿ ‫َوَلُهم َعَذاٌب َأِليٌم ِبَما َكاُنوا َيْكِذُبوَن‬

"Kuma suna da azaba mai radadi abisa abinda suke


ƙaryatawa". (Al-Baƙara:8-10)

Kitāb ʿAqīdah at-Tawḥīd na Shaykh Ṣāliḥ Al-Fawzān (sh. 44)

6. Ikhlasi (Al-ikhlāṢ) :

Shi ne tsarkake zuciya daga dukkan wasu datti na shirka.


Kada ya nufaci wani abu na duniya idan ya furta (Lā ilaha ilā
Allāh) babu riya ko neman suna saboda abinda yazo a
hadisi ingantacce, Hadisin itbaan yace:

"Lalle Allāh ya haramta wuta ga duk wanda yace Lā ilaha -


ilā Allāh yana neman yarda Allāh da hakan". (Bukhārī da
Muslim)

Kitāb ʿAqīdah at-Tawḥīd na Shaykh Ṣāliḥ Al-Fawzān (sh. 44)

7. So (Al- maḥ abbah) :

Son wannan kalmar da ma'anarta, da son ma'abotanta


masu aiki da ita. Allāh, Madaukakin Sarki, yace:

‫َوِمَن الَّناِس َمن َيَّتِخُذ ِمن ُدوِن الّلِه َأنَدادًا ُيِحُّبوَنُهْم َكُحِّب الّلِه َواَّلِذيَن آَمُنوْا‬
﴾١٦٥﴿ ‫َأَشُّد ُحًّبا ِّلّلِه‬

"Daga cikin mutane akwai wanda yake riqar kishiyoyi yana


sonsu kamar yadda yakeson Allāh, wadanda sukayi imani
kuwa suna tsananin so ga Allāh". (Al-Baƙara:165)

-Ma'bota Lā ilaha ilā Allāh suna yiwa Allah tataccen so.

-Ma'abota Shirka suna son Allah kuma suna son waninsa.


Wannan kuma yana kore abinda Lā ilaha ilā Allāh take
hukuntawa.

Kitāb ʿAqīdah at-Tawḥīd na Shaykh Ṣāliḥ Al-Fawzān (sh. 45)

Você também pode gostar